Obasanjo ya tambayi Buhari kan isalin sayen gidan sauro

Obasanjo ya tambayi Buhari kan isalin sayen gidan sauro

- Obasanjo ya tambayi Buhari ya isalin $16m na sayen gidan sauro, ko ina maganar ta kwana

- Tsohon shugaban kasar yayi yabo ga uwargidan shugaba Muhammadu Buhari saboda kasancewar tana fadin gaskiya kan kusakuran gwamnatin maigidanta

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi yabo ga uwargidan shugaba Muhammadu Buhari saboda kasancewar tana fadin gaskiya kan kusakuran gwamnatin maigidanta

Obasanjo yace: “Nayi matukar farin ciki ganin cewa matar shugaban kasa na magana. Ba shakka tana kokari kwarai da gaske, ina ganin akwai bukatar ta tattauna da shugaban kasa yayin da suka ja labule.”

Uwargidan shugaban kasa na kokari kwarai da gaske wurin fadin gaskiya duk da cewa tana cikin wannan mulkin da ake a yanzu. Idan ta ga kuskure tana magana domin ya kasance an samu gyara kafin abin ya haifar da babbar matsala.

KU KARANTA:Duka biyu: Gobara ta cinye kayan tallafin yan gudun hijira a jahar Borno

“Hakika, ta jima tana fadin gaskiya zuwa ga gwamnatin tarayya wacce maigidanta ke shugabanta. Amma ni abinda ta fadi a kwanakin nan ana daf da rantsar da maigidanta a zangonsa na biyu ne ya janyo hankalina, inda ta caccaki gwamnati kan sayen gidan sauro.”

A wurin taron da Aisha Buhari ta shirya domin mata zalla ta fadi kudi dala miliyan goma sha shida ($16) a matsayin wanda aka ware domin sayen gidan sauro.

A kalamanta cewa tayi, “ Na samu labarin Najeriya ta biya $16m domin sayen gidan sauro, ni kuma na nemi su bani gidan sauron in kai kauyenmu amma ba’a bani ko daya ba.

“ An kashe $16m domin sayen gidan sauro, ni dai ban samu ko daya ba ba mamaki wasu sun samu. Ko da yake ina ganin wannan ra’ayine nawa na karon kaina amma $16m ta isa mu yi feshin maganin sauro a fadin kasar nan lungu da sako.” A cewarta.

"Wannan magana da Aisha tayi na kunshe da sakonni guda biyu, na farko shi ne; laifin cin hanci da rashawa tare da almubazaranci da dukiya. Na biyu kuma shine akwai lauje cikin nadi musamman a bangaren harkokin da suka shafi kula da muhalli.” Inji Olusegun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel