Wani mutumi yayi wa matarsa dukan kawo wuka saboda tayi masa wata tambaya akan karuwarshi

Wani mutumi yayi wa matarsa dukan kawo wuka saboda tayi masa wata tambaya akan karuwarshi

Wani mutumi ya yiwa matarsa dukan kawo wuka bayan tayi korafi akan sakon bikin murnar ranar haihuwar da karuwarshi ta turo masa ta wayar salula

A cewar wata mata da take amfani da manhajar Instagram mai suna @yommigold ta sanya labarin a shafinta na Instagram, inda ta bayyana cewa matar wacce ba a bayyana sunanta ba ta tambayi mijin nata dalilin da ya sanya karuwar tashi ta turo masa sakon murnar ranar haihuwa, inda take cewa: "Happy happy birthday my husband" a turance.

Matar wacce ta sanya labarin ta kuma yi wani rubutu kamar haka:

"Mijinta yayi mata dukan tsiya kawai saboda ta tambayeshi dalilin da ya sanya wata karuwa ta turo mishi sakon murnar ranar haihuwa, a cewarta, mijin ya daki kanwarta da kuma 'yarsu a lokacin da suka zo domin su kwaci matar."

KU KARANTA: 'Yan sanda sunyi nasarar ceto mutane 20 a hannun wani matsafi da yake amfani da jininsu

Kwanan nan ne maajiyarmu Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda wani limamin coci Funke Felix Adejumo ya sanya kace-nace a kafafen sada zumunta, bayan an nuna shi a wani bidiyo yana shawartar mata akan cewa kada wacce ta damu idan mijinta yana zuwa yana kwanciya da wata a titi.

Bidiyon yana fadakarwa ne akan kada mata su dauki damuwa su sanyawa kansu idan suka fahimci cewa mijinsu yana biye-biyen mata a titi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel