'Yan sanda sunyi nasarar ceto mutane 20 a hannun wani matsafi da yake amfani da jininsu

'Yan sanda sunyi nasarar ceto mutane 20 a hannun wani matsafi da yake amfani da jininsu

- Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta gano wata maboyar 'yan kungiyar asiri

- Rundunar ta ceto mutane 20 daga hannun 'yan kungiyar asirin

- Sannan rundunar ta kama wani mai suna Alfa Oloore wanda yake da hannu wurin aikata ta'addanci

Kimanin mutane 20 aka kubutar daga daga gidan wasu 'yan kungiyar asiri a yankin Agungun cikin birnin Ibadan jihar Oyo.

Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa rundunar 'yan sandan jihar ne suka binciko maboyar bayan wani rahoton sirri da aka kai musu.

Da yawa daga cikin mutanen da aka ceto yunwa ta rika ta gama cinye musu jiki, saboda rashin abinci.

Rundunar kuma ta samu nasarar cafke daya daga cikin 'yan kungiyar asirin mai suna Alfa Oloore.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa mutumin wanda ya nuna cewa shi mai magani ne ya jima yana zaune a gurin, inda suke ta zargin cewa bashi da gaskiya.

KU KARANTA: PDP ta caccaki shugaba Buhari akan furucin da yayi kan mazauna Abuja

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Gbenga Fadeyi ya tabbatar da kama mutumin.

Haka kuma, Shehu Lawal, mataimakin shugaban hukumar 'yan sanda na yankin jihar Legas da Ogun ya tabbatar da cewar rundunar yanzu a shirye take domin tinkarar makiyaya da masu satar mutane a fadin jihar.

Lawal, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana wasu masu laifi a helkwatar 'yan sanda ta jihar Legas, ya gargadi makiyaya da suke da tunanin aikata laifi a yankin jihar Legas da Ogun.

Majiyarmu ta kawo muku cewa shugaban hukumar 'yan sanda ya bayyana cewa matsalar makiyaya ta shafi kowa da kowane a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel