PDP ta caccaki shugaba Buhari akan furucin da yayi kan mazauna Abuja

PDP ta caccaki shugaba Buhari akan furucin da yayi kan mazauna Abuja

- Bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki mazauna garin Abuja saboda basu zabe shi ba a zaben da ya gabata

- Jam'iyyar PDP ta fito ta bayyana rashin jin dadinta akan irin furucin da shugaban kasar yayi akan al'ummar birnin tarayyar

- Jam'iyyar ta bayyana cewa bai kamata shugaban kasa ya dinga irin wannan furuci na batanci akan al'ummarsa ba

Shugabannin jam'iyyar PDP sun kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da ya kira mazauna babban birnin tarayya da "Masharranta" saboda basu zabe shi ba a lokacin zaben da aka gabatar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Yayin da yake taro da wasu 'yan Najeriya saboda murnar karamar sallah ranar Talata, shugaban kasar ya kira mazauna Abuja da "Masharranta" saboda basu zabe shi ba.

Amma yayi alkawarin kwatanta adalci a garesu, duk da cewa basu zabe shi ba.

KU KARANTA: PDP na zagon kasa don ruguza jam'iyyar APGA - In ji shugaban jam'iyya

A wata sanarwa da ta fito daga bakin kakakin jam'iyyar Kola Ologbondiyan, PDP ta bayyana cewa irin wannan maganar da Buhari yayi bai kamata ba a siyasance, saboda kowa a Najeriya yana da damar da zai zabi duk abinda yake so.

Babbar jam'iyyar adawar ta bayyana furucin shugaban kasar a matsayin, wanda yake kokarin ganin ya rarraba kan jama'a da kuma sanya mutane su dinga yi musu wani kallo na daban.

Jam'iyyar ta kuma nuna bacin ranta akan maganar da yayi, inda yake cewa "don bayar da tsaro a Abuja dole sai na bai wa kaina da mataimakin shugaban kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel