APC: Ya zama wajibi Oshiomole yayi ritaya saboda gudun matsala, inji ministan Buhari

APC: Ya zama wajibi Oshiomole yayi ritaya saboda gudun matsala, inji ministan Buhari

- Rikici na cigaba da aukuwa a tsakanin 'yan yan jam'iyar APC inda da dama ke neman shugaban jam'iyar na kasa da yayi murabus kan ya kashe jam'iyar ta APC.

- Tsohon ministan sadarwa Adebayo Shittu shi ne yayi wannan nuni yayin wata zantawa da yayi da jaridar Premium Times.

Rashin gaskiya da nuna son kai na shugaban APC ne ya janyo jam’iyar tayi hasarar jihar Oyo da ma wasu jihohin a zaben da ya gabata a kasar nan, a cewar tsohon ministan sadarwa Adebayo Shittu.

Da yake zantawa da jaridar Premium Times ranar Litinin a Abuja, Shittu ya shiga cikin jerin masu neman Oshiomole yayi ritaya daga kujerarsa.

KU KARANTA:Duka biyu: Gobara ta cinye kayan tallafin yan gudun hijira a jahar Borno

Ya ce, “Ya zama wajibi Oshiomole yayi murabus domin kaucewa baraka a zaben 2023.” Wannan zancen da ministan yayi ya biyo bayan matsalar da ya fuskanta daga bangaren jam’iyar APC bisa hana shi tsayawa takarar gwamna a jihar Oyo."

Ministan ya cigaba da cewa, “Mara gaskiya ko a ruwa yake tilas sai yayi gumi, ramin karya kuma kurarre ne.” Kwamitin zartarwa na APC karkashin jagorancin Oshiomole ne ya dakatar da Shittu daga takarar gwamnan kasancewar baiyi bautar kasa ta NYSC ba wacce take wajibi a kasar nan.

“Ko shakka babu gaskiya tayi halinta a jihar Oyo, Allah ya nuna wa jagororin APC ikonsa. Babu yadda za’ayi kayi wa mutane tilas akan rashin gaskiya.” A cewarsa.

Ya kara da cewa, “an dakatar dani kan dalilin cewa banyi NYSC ba duk da cewa kotu ta ban kariyar cewa zan iya tsayawa takarar. Zance na gaskiya shine abokin takarata ma gwamna Abiola Ajimobi bai yi bautar kasan ba.”

Shittu yace, “ wannan ba shi bane karo na farko da aka nuna min rashin gaskiya. An taba hana ni takara a jam’iyar Unity Party of Nigeria UPN kan na fadawa jam’iyar gaskiya bisa rashin adalcin su.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel