Sallah: An kashe bako a fadar Sarkin Kano, an jikkata da dama a hawan Daushe

Sallah: An kashe bako a fadar Sarkin Kano, an jikkata da dama a hawan Daushe

Tashin hankali ba’a sa maka rana ini masu iya magana, wannan shine kwatankwacin abinda ya faru a kofar fadar mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a yayin hawan Sallah a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni.

Jaridar Guardian ta ruwaito rikici ya barke a kofar fadar da misalin karfe 7 na dare yayin da aka kammala gudanar da hawan Sallah, sakamakon wasu kungiyoyin matasa masu hamayya da juna da suka far ma kawunansu.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kama hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

Sallah: An kashe bako a fadar Sarkin Kano, an jikkata da dama a hawan Daushe

Hawan Dawakai
Source: Twitter

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da fari kamar da gaske ana ta hawa ana sukuwa akan dawakai cikin farin ciki, nuna murna da nishadi, amma da misalin karfe 7 na dare ne wasu miyagun matasa suka kutsa kai cikin taron da nufin tayar da hankali.

Sai dai fadawan Sarki da mafarauta sun yi kokarin taka ma miyagun burki, inda hakan ya janyo sare sare tare da jefa muggan makamai a cikin jama’a sakamakon haka taron ya fashe kowa yayi ta kansa, a dalilin haka aka kashe mutum daya tare da jikkata wasu yan kallo da dama.

Ba tare da wata wata ba jami’an tsaro suka yi ma Sarki Sunusi II shinge, tare da hakimansa dama saura manya manyan bakin da aka gayyato daga kasashen waje domin suyi kallon hawa, a haka aka tseratarsu dasu duka.

Sai dai gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bai samu damar halartar hawan daushen ba, inda ya tafi sabuwar masarautar Bichi domin kallon hawan sabon Sarki mai daraja ta daya, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna, game da lamarin, inda shi da kansa ya tabbatar da aukuwar mummunan rikicin, sai dai yace bashi da tabbacin adadin mutanen da rikicin ya shafa.

Da wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya bada umarnin soke hawan Nassarawa da Sarkin Kano zai gudanar a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, inda yace gwamnati ta samu rahotanni tsaro daga hukumomin tsaro dake nuna da sauran rina a kaba, akwai masu shirin tayar da hankali a yayin hawan.

Haka zalika shima Sarki Sunusi ya yi biyayya ga wannan umarni na gwamna, inda ya soke gudanar da wannan hawa domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel