PDP na zagon kasa don ruguza jam'iyyar APGA - In ji shugaban jam'iyya

PDP na zagon kasa don ruguza jam'iyyar APGA - In ji shugaban jam'iyya

- Jam'iyyar APGA ta koka da irin munafurcin da jam'iyyar PDP keyi a jihar Abia domin ganin ta raba kan 'yan jam'iyyar ta

- Ta ce ta dauki hayar tsohon shugaban jam'iyyar domin ganin ta kawo karsehn jam'iyyar a fadin jihar

Jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA), ta jihar Abia tayi zargin cewa babbar jam'iyyar adawa ta PDP tana daukar 'yan jam'iyyarta a boye domin ta ruguza jam'iyyar a fadin jihar.

Da yake magana da manema labarai a Umuahia, sabon shugaban jam'iyyar APGA na jihar Abia, Cif Nkem Okoro, ya ce wasu daga cikin mutanen da suke daukar kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar APGA, jam'iyyar PDP ce ta dauke su haya domin su ruguza jam'iyyar a fadin jihar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari: Abinda yasa na danka dukiyar kasar nan a hannun mata

Jam'iyyar ta bayyana cewa PDP na tsoron karar da APGA ta kai kotu akan magudin zabe, shine yasa ta dauki hayar tsohon shugaban jam'iyyar domin raba kan jam'iyyar a fadin jihar.

Okoro wanda ya bayyana jam'iyyar APGA a matsayin babbar jam'iyyar adawa a jihar, ya bayyana cewa sababbin 'yan kwamitin jam'iyya guda 26 da aka zaba zasu mayar da hankali wurin dawo da martabar jam'iyyar.

Sabon shugaban jam'iyyar ta APGA ya yaba da kokarin Dr. Alex Otti, inda ya bayyana cewa ya kawo shugabanni na gari da zasu kawo cigaba ga jam'iyyar a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel