Shugaba Buhari: Abinda yasa na danka dukiyar kasar nan a hannun mata

Shugaba Buhari: Abinda yasa na danka dukiyar kasar nan a hannun mata

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wasu dalilan shi da ya sanya ya mika dukiyar kasar nan a hannun mata

- Shugaban ya kuma yi alkawarin bai wa mata manyan mukamai a fadin kasar nan

- A karshe an yiwa shugaban addu'ar Allah ya kara masa lafiya da karfin gwiwar gabatar da abubuwan alkairi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sanya ya danka baitulmalin kasa a hannun mata.

Shugaban kasar yayi bayanin ne a lokacin da ya hada wani taron shan ruwa ga mata a fadar shi dake Abuja, shugaban ya bayyana cewa zai bai wa mata mukamai da yawa a wannan sabuwar gwamnatin.

"Ina ganin abinda ya fi ga kowanne shugaba, shine ya mika dukiyar kasa a hannun mace, ko da kuwa a gida ne ko a ofis. Tun lokacin dana hau mulki mata ne ke rike da dukiyar kasar nan.

KU KARANTA: Boko Haram: Abubuwan da Shekau ya ce a sabon bidiyon da ya fitar

"Saboda haka ban tunanin dole sai namiji ne zai rike dukiyar kasa, abu mafi muhimmanci shine wanda yafi iya aiki da tsoron Allah. Ku duba dukiyar kasar nan kuma ku duba yadda ma'aikatun kasar nan suke," in ji shi.

Wacce ta shugabanci matan, babbar mai taimakawa shugaban kasa ta musamman, Dr. Hajo Sani, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya mata da yawa a cikin wannan sabuwar gwamnati tashi.

Hakazalika, ita ma da take bayani tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Filato, Pauline Tallen tayi adduar Allah ya karawa shugaban kasa lafiya, da karfin gwiwa akan dukkan abinda ya sanya gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel