Duka biyu: Gobara ta cinye kayan tallafin yan gudun hijira a jahar Borno

Duka biyu: Gobara ta cinye kayan tallafin yan gudun hijira a jahar Borno

Da sanyin safiyar Laraba, 5 ga watan Yuni ne wata mummunar gobara ta tashi inda ta kone wasu kayayyakin tallafi da aka sayo ma yan gudun hijiran dake tsugune a sansanonin yangudun hijira a jahar Borno.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan gobara dai ta tashi ne a katafaren dakin ajiyan kayayyakin tallafi na kwamitin shugaban kasa dake agaza ma jama’an yankin Arewa maso gabas, PCNI, dake titin Baga cikin garin Maiduguri.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya musanta zargin almubazzarantar da naira biliyan 3.4

Wutar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar Laraba, inda ta kone akalla katifun barci guda 400, motar daukan kaya guda daya da kuma sauran kayan abinci da ma kayayyakin amfanin yan gudun hijira.

Sai dai anyi sa’a jami’an hukumar tsaro ta farin kaya na Civil Defence dana hukumar kashe gobara sun isa wurin da gaggawa, inda suka yi kokarin kashe gobarar, tare da dakatar da ita daga wanzuwa zuwa wasu sassa.

Kaakakin hukumar kashe gobara ta jahar Borno, Ambursa Pindar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sun girke motar kashe gobara guda daya a wajen, sa’annan yace ya tabbatar da babu wanda ya mutu ko ya jikkata a sanadiyyar gobarar.

“Amma dai har yanzu mun kasa gano musabbabin tashin gobaran sakamakon babu kowa a farfajiyar gidan ajiyan kayayyaki, babu masu gadi babu jami’an kwamitin, babu kowa.” Inji shi.

Sai dai da aka tuntubi shugaban sashin watsa labaru da sadarwar na kwamitin PCNI, Alkasim Abdulkadir sai ya kada baki yace “Har yanzu babu wanda yayi min bayani game da gobaran, don haka bani da masaniya game da ita.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel