Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashe 'yan Boko Haram da dama

Harin kwanton bauna: Dakarun soji sun kashe 'yan Boko Haram da dama

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun kai wa mayakan kungiyar Boko Haram harin kwanton bauna a Arewacin Borno inda suka kashe masu yawa daga cikinsu.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin, Kwanel Sagir Musa ya bayar da ta ce an kwato bindigu da sauran makamai daga hannun 'yan ta'addan.

Kwanel Musa ya ce: "Sakamakon bayyanan sirri da wasu 'yan kasa na gari suka bawa soji kan harin da aka shirya kaiwa batalliyar 114, E Company da ke kauyen Izge a karamar hukumar Gwoza na jihar Borno, Dakarun 143 battalion sun kai wa 'yan ta'addan harin kwanton bauna a hanyar kauyen Kubu a ranar 4 ga watan Yunin 2019.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

"'Yan ta'addan sun fada tarkon da sojojin suka dana musu wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar da yawa cikinsu da kuma kwato makamai da suka hada da: Bindiga AK 47 guda 4, 81 Millimetre Mortar guda 1, wasu makamai na daban-daban, Motocci kirar Hilux 2, Injin janyo ruwa.

"Babu wanda ya mutu a bangaren sojojin sakamakon harin.

"Rundunar Sojin tana amfani da wannan damar ta bakin Operation Lafiya Dole wurin mika godiya da jinjina ga wadanda suka bawa sojojin bayannan sirrin da ya yi sanadiyar kashe 'yan ta'addan tare da kira da mutane su rika gaggawar bawa hukumomin tsaro bayannai masu amfani domin magance 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka a Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel