Sarki Sanusi ya bi umarnin Ganduje, ya soke hawan Nasarawa

Sarki Sanusi ya bi umarnin Ganduje, ya soke hawan Nasarawa

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soke hawan Nasarawa da aka saba yi duk lokacin bikin karamar sallah bisa umarnin gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Laraba ne gwamna Ganduje ya umarci sarki Sanusi da ya fasa hawan Nasarawa saboda wasu dalilian tsaro.

A jawabin da mukaddashin sakataren masarautar Kano ya fitar, sarki Sanusi ya yi biyayya ga umarnin gwamnan tare da rokon jama'a su kwantar da hankalinsu.

Dangane da soke hawan, masarautar Kano ta ware ranar 7 ga wata domin gudanar da addu'o'i na musamman domin tuna wa da cika shekaru biyar da mutuwar tsohon sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, da kuma bikin cikar Sanusi shekaru biyar a kan mulki.

Sarki Sanusi ya bi umarnin Ganduje, ya soke hawan Nasarawa

Sanusi da Ganduje
Source: UGC

Jaridar Daily Nigerian ta ce ta samu labarin cewar gwamnatin Kano ta soke hawan ne saboda takun sakar dake tsakanin sarkin Sanusi da gwamna Ganduje.

DUBA WANNAN: Buhari ya soki masu yiwa talakan Najeriya bukulu a mulkinsa

Gwamnatin Kano ta saka kafar wando daya da masarauta ne bisa zargin cewar sarki Sanusi na goyon bayan dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, a aben da ya gabata.

Domin rage karfin da sarki Sanusi ke da shi, gwamna Ganduje ya kirkiri sabbin masarautu hudu a Kano wadanda suka hada da Bichi, Rano, Gaya da Karaye.

Duk da wata kotu ta yi kokarin dakatar da gwamnan, ya yi burus da umarnin ta ya nada sabbin sarakunan yanka tare ba su sandar iko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel