Yanzu Yanzu: Ganduje ya soke hawan Nasarawa a Kano

Yanzu Yanzu: Ganduje ya soke hawan Nasarawa a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta soke Hawan Nassarawa da za a gudanar a ranar Alhamis 6 ga watan Yunin 2019 saboda dalilan tsaro.

An bayar da sanarwar soke hawan ne a jiya bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki a fannin tsaro inda akayi bita kan hawan sallar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na gwamna, Alhaji Abba Anwar ya nuna cewa majalisar tsaro ta Kano ta samu bayannan sirri da ke nuna yiwuwar tayar da fitina yayin hawan na sallah.

Sanarwar ta kuma bayyana cewar an sanar da masarautar Kano matakin da gwamnatin ta dauka.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

An bukaci al'umma su cigaba da gudanar da harkokinsu yadda suka saba domin an dauki matakan tsare rayuka da dukiyoyin su.

"Bayan taron taron tsaro da aka gudanar tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da hukumomin tsaro a kan bukukuwar sallah kamar yadda aka saba, an samu bayyanan sirri da ke nuna akwai yiwuwar tayar da fitina.

"Kamar yadda aka sani, Gwamna Ganduje mutum ne mai son zaman lafiya da baya wasa da tsaron al'ummar Kano.

"Saboda wannan dalilin da kuma bayyanan sirrin da aka samu, gwamnatin jihar ta soke Hawan Nassarawa.

"Bayan taron an sanar da masarautan Kano kan mummunar bayyanan sirrin da kuma matakin da aka dauka na soke Hawan Nassarawa," inji sanarwar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel