Boko Haram: Abubuwan da Shekau ya ce a sabon bidiyon da ya fitar

Boko Haram: Abubuwan da Shekau ya ce a sabon bidiyon da ya fitar

Jagoran 'yan kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya kara sakin wani sabon faifan bidiyo, inda yake bayyana irin akidar kungiyar tasa sannan kuma yayi Allah wadai da tsarin mulki irin na dimokradiyya

Faifan bidiyon da ya fitar wanda yake da tsawon minti 35 da dakika 37 ya bayyana Shekau a matsayin jagoraan kungiyar Jama'at Ahlul Sunna Lil-Da'wah wal-Jihad.

A faifan bidiyon, Shekau ya bayyana a zaune da kaya farare da kuma bindiga kirar AK47 a rataye a kafadarsa, sannanan nuna shi yana karanto jawabin nasa daga wata takarda dake hannunsa.

A jikin bidiyon an nuna tutar kungiyar Boko Haram. Sannan an nuna wasu mutane biyu dauke da bindigogi sun boye fuskokinsu a cikin bidiyon.

Sai dai kuma alamu na nuna cewa ya samu matsalar ido, ganin yadda yake ta fama a lokacin da yake karanto takardar tasa.

KU KARANTA: An kai hari wani Masallaci, daidai lokacin da mutane ke sallar Idi

Duk da dai har yanzu babu wani cikakken bayani dake nuna ainahin lokacin da aka fitar da bidiyon, amma a jikin kwanan watan dake jikin bidiyon ya nuna cewa an saki bidiyon ranar 6 ga watan Mayun da ya gabata ne.

A bayanin da Shekau din yayi ya bayyana cewa babban burinsa shine ya samu magoya baya daga wurin 'yan Najeriya.

Shekau yace kungiyarsa na bin sunna ne wacce ita ce "ingantacciyar akidar musulunci", kuma ita ya kamata kowanne musulmi ya bi.

Ya kuma kara da cewa duk al'ummar dake bin addinin Yahudawa da addinin Kirista to jininsu ya halatta a gurinsu.

A karshe Shekau ya maimaita adawarsa akan irin tsarin karatun Boko na Turawan yamma da ake koyawa a makarantun Najeriya, inda ya bayyana hakan a matsayin kafirci da sabon Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel