Sojoji sunyi luguden wuta a sansanin Boko Haram da ke Tumbun Kaiyowa

Sojoji sunyi luguden wuta a sansanin Boko Haram da ke Tumbun Kaiyowa

Rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole sun tarwatsa sansanin 'yan Boko Haram da motoccin su da garin Tumbun Kaiyowa da ke Arewacin Borno.

Direktan yada labarai da hulda na mutane na NAF Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayar da sanarwar a ranar Laraba a Abuja inda ya ce an kai harin ne a ranar Laraba.

"An kai harin ne bayan anyi amfani da jiragen leken asiri wurin tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun samu mafaka a wurin tare da kayayakin isar da sakonninsu da wasu gine-ginen da ke cikin dokar daji.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

"Dakarun sojojin saman sun aike da jiragen yaki biyu kirar Alpha Jet inda suka kai hari kan gine-ginen 'yan ta'addan kuma su kayi nasarar kone wurin kurmus.

"Dakarun kungiyar ta'adda na ISWAP da dama sun mutu sakamakon harin saman da aka kai," inji shi.

Kakakin na NAF ya ce sojojin da sauran jami'an tsaro za su cigaba da yiwa 'yan ta'addan luguden wuta har sai an ga bayan su a yankin na Arewa maso Gabas kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel