An kai hari wani Masallaci, daidai lokacin da mutane ke sallar Idi

An kai hari wani Masallaci, daidai lokacin da mutane ke sallar Idi

- Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai wani Masallacin Idi a kasar Afganistan

- Bayan mutuwar mutane biyun, akwai sama da mutane 12 da suka ji munanan raunika

- An sanya bam dinne a jikin wani babur aka ajiye shi a bakin kofar masallacin

Rayukan mutane biyu ne ya salwanta saboda wani harin bam da aka kai wani babban Masallacin Idi a daidai lokacin da al'umma ke gabatar da sallar Idi a yankin Nahrain dake cikin jihar Baglan kasar Afganistan.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Baglan Ahmet Jawid Basharat ya bayyana cewa, bam ya tashi ne a jikin wani babur wanda aka daura shi aka ajiye a bakin kofar shiga Masallacin.

Basharat ya bayyana cewa mutane biyu ne suka rasa rayukansu a dalilin tashin bam din, sannan kuma sama da mutane 12 sun ji munanan raunuka.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya hana Tinubu fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Jigo a APC

Har ya zuwa yanzu dai babu wani wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, kuma hukumar tsaron kasar har yanzu bata gano wanda ya sanya bam din ba.

A Najeriya ma wasu da ake tunanin 'yan bindiga ne sun kai hari wani Masallaci a garin Maiduguri daidai lokacin da mutane ke yin sallar Tahajjud, hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, sannan da dama sun jikkata dalilin kai harin.

Ana ta fama da matsalar rashin tsaro a wasu sassa na kasashen duniya, musamman ma yankin kasashen nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel