Babu wanda ya isa ya hana Tinubu fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Jigo a APC

Babu wanda ya isa ya hana Tinubu fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Jigo a APC

- Moshood Salvador, jigo a babbar jam'iyya mai mulki APC, ya ce babu wani mutumi da ya isa ya dakatar da Asiwaju Bola Tinubu fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2023

- Haka kuma Salvador ya caccaki Afenifere wanda yace a mikawa yankin kudu maso gabas kujerar shugabancin kasar

- Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya bukaci Afenifere ya mayar da hankali wurin nemo mafita ga kalubalen dake damun Najeriya

Babu wanda ya isa ya hana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu fitowa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC mai mulki a shekarar 2023, jigo a jam'iyyar APC, Moshood Salvador shine ya bayyana hakan.

Salvador ya bayyana hakan ne a wani gargadi da yake yiwa Afenifere, da wasu manya na kabilar Yarabawa wadanda suke kokarin kawo cikas a yunkurin da yake yi.

Jigon jam'iyyar APC ya ce duk wanda suke kokarin ganin sun kawo cikas akan abinda Tinubu ya sanya gaba to su tabbata da cewa tun yanzu sun fadi.

KU KARANTA: Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Fasto

Jaridar This Day ta bayar da rahoton cewa jigon ya bayyana cewa babu wani wanda ya isa ya dakatar da shi fitowa takarar tunda har Allah ya yadda dashi.

Ya bayyana cewa bai kamata ba ace shugabanin Yarabawa su nuna rashin amincewarsu wurin fitowarsa takarar a wannan yanki. Ya bayyana hakan a matsayin rashin kishi.

Salvador yace maimakon su dinga jayayya akan takarar tashi kamata yayi ace su zauna su nemo mafita akan matsalolin dake damun yankin Yarabawa dama kasa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel