Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifiyar wata tsohuwar yar majalisa

Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifiyar wata tsohuwar yar majalisa

Masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifiyar wata tsohuwar yar majalisar dokokin jihar Bayelsa, Kate Owoko mai shekara 78 a duniya.

An tattaro cewa masu garkuwan sun yasar da gawar mahaifiyar yar majalisar a kogin Amassoma, karamar hukumar kudancin Ijaw.

An rahoto cewa yan bindigan sun sace matar a gidanta da ke Amassoma, garin marigayi tsohon gwamnan Bayelsa, Diepreye Alamieyeiseigha a ranar 18 ga watan Afrilu.

Masu garkuwan sun tsare marigayiyar kusan watanni biyu da suka gabata bayan sabani da suka samu da yan uwanta akan kudin fansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Butswat Asinim, ya tabbatar da lamarin inda ya bayyana hakan a matsayin abun bakin ciki.

Yace yan sanda na kokarin ganin sun ceto tsohuwar kafin a gano gawarta a gefen kogi.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Ghana a Abuja (hotuna)

Asinim yace yan sanda za su yi iya bakin kokarinsu domin kama wadanda suka aikata ta’asan sannan su hukunta su.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sanda a jihar Bauchi sun kama wasu mutane hudu da ake zargin yan fashi da makami ne da kuma yan Sara-Suka 60 a fadin jihar. An gurfanar da masu laifin ne a hedkwatar rundunar da ke Bauchi.

A cewar kakakin yan sandan, DSP Kamal Datti Abubakar, anyi kamun ne duk a cikin kokarin da kwamishinan yan sandan jihar, CP Habu Sani Ahmadu, ke yin a kawar da yan ta’adda a jihar.

Ya bayyana cewa tawagar rundunar na Operations Puff Adder ne suka kama yan fashin ne a ranar 2 ga watan Yuni, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel