Gwamnatin Tarayya ta fara shirye shirye akan kasafin kudin 2020

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye shirye akan kasafin kudin 2020

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta daura damarar fara shirye shirye akan kasafin kudin kasar nan na 2020 inda ta bayar da umurnin alkinta dukiya ga ma'aikatu da kuma cibiyoyin gwamnati.

Gwamnatin ta kuma gindaya gargadi na jan kunnen shugabannin ma'aikatu da kuma cibiyoyin gwamnati a kan sanya sunayen ma'aikatan bogi cikin sahun masu karbar albashi domin kuwa ba za ta rangwanta wa duk wanda aka samu da wannan mummunan laifi ba.

Wannan gargadi ya zo a cikin wata takardar sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar na bayyana shirye shiryen ta akan kasafin kudin kasa na 2020 wadda ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Satana Udomo Udo Udoma ya rattaba wa hannu.

Ministan ya aike da takardar sanar da shirye-shiryen kasafin kudin 2020 a ranar 24 ga watan Mayun 2019 zuwa ga shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da kuma mataimakin sa, sakataren gwamnatin tarayya, shugabannin hukumomin tsaro da kuma sufeto janar na 'yan sanda.

KARANTA KUMA: A kebance kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa zuwa Arewa maso Yamma - Sanata Kabiru Gaya ya gargadi APC

Sauran wadanda takardar ta isa gare su sun hadar da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Ciyamomin hukumomin gwamnati, manyan sakatarori gwamnatin tarayya da kuma shugabannin rassan ma'aikatun gwamnati.

Jaridar The Punch bayan samun damar hangawa cikin takardar da ministan ya aike da ita, ta bayar da shaidar cewa, akwai muhimmiyar bukatar fara gudanar da shirye shirye a kan kasafin kudin 2020 domin alkinta dukiyar kasar nan gwargwadon iko.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel