'Yan sanda sun kama gaggan 'yan fashi da makami 4 a Bauchi

'Yan sanda sun kama gaggan 'yan fashi da makami 4 a Bauchi

Rundunar 'Yan sanda na Jihar Bauchi sun kama wasu mutane hudu da ake zargin 'yan fashi da makami ne inda aka kwato mota kirar Lexus Jeep 2007 da aka sace daga unguwar Kofar Gombe a garin Bauchi.

An kama wadanda ake zargin ne sakamakon bayannan sirri da tawagar 'yan sanda na Operation Puff Adder suka samu.

'Yan fashin sun hada da: Audi Daniel mai shekaru 29 dan asalin karamar hukumar Gboko a jihar Benue da John Samuel mai shekaru 22 dan asalin karamar hukumar Olu da ke Jihar Imo.

An kama mutane biyun na a Kofar Gombe da ke garin Bauchi a ranar 2 ga watan Yunin 2019.

Sauran 'yan kungiyar fashin sun hada da Ikenna Okoronko mai shekaru 28 daga karamar hukumar Janta na jihar Plateau da Solomon Ijika mai shekaru 32 da ke zaune a Federal Low cost da aka kama a ranar 3 ga watan Yuni bisa zarginsu da hannu cikin fashin.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Rundunar 'yan sandan ta ce an gudanar da bincike mai zurfi kafin aka samu nasarar kama su.

A yayin da ya ke tabbatar da kama su a ranar Laraba, Kakakin 'yan sanda, DSP Kamal Datti ya ce an kama 'yan fashin ne kwazon da kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Habu Sani Ahmadu ya ke yi na kokarin kawar da miyagun ayyuka.

Ya ce: "Dakarun 'Yan sanda na Operation Puff Adder sun kama wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne a Kofar Gombe kuma sun kwato mota kirar Lexus Jeep RX 350, kirar 2007 mai launin ruwan toka mai lambar chasis 2T2GK31U37100 da lambar rajista EPE 734 EU da kudin ta ya kai naira miliyan 4 bayan samun bayyanan sirri."

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa sun yiwa mai motar fashi tare da wasu mutane uku a wani daji da ke hanyar Abuja zuwa Jos.

Kayayakin da aka samu a hannun 'yan fashin sun hada da wayar salula kirar infinix mallakin mai motar, takardun mota dauke da sunan wata Linda da ke zaune a No. 51 Rukuba Jos, Jihar Plateau da wasu tufafi da sarkan wuya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel