Majalisar Wakilai za ta gudanar da zaman ta na bankwana a ranar Alhamis

Majalisar Wakilai za ta gudanar da zaman ta na bankwana a ranar Alhamis

Majalisar wakilai ta takwas a tarihin dimokuradiyyar Najeriya, za ta kawo karshen duk wasu nauye nauye da suka rataya a wuyan ta a taron bankwana yayin zaman da za ta gudanar a gobe Alhamis, 6 ga watan Yunin 2019.

Mukaddashin mai rikon sandar iko ta majalisar wakilai, Patrick Giwa, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanar a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Laraba cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Cikin sanarwar da Honarabul Giwa ya bayyana, ya ce majalisar wakilai ta tarayyar kasar nan za ta fara gudanar da zaman ta na bankwana da misalin karfe 11.00 na safiyar ranar Alhamis a zauren majalisar dake garin Abuja.

KARANTA KUMA: Kotu ta yankewa malamin Shi'a hukuncin dauri na shekaru 2 a kasar Faransa

An bukaci dukkanin 'yan majalisar da kuma manyan baki su kasance sun samar wa kawunan su matsugunni tun misalin karfe 10.30 na safiyar Alhamis gabanin fara gudanar da zaman gadan gadan kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel