Kotu ta yankewa malamin Shi'a hukuncin dauri na shekaru 2 a kasar Faransa

Kotu ta yankewa malamin Shi'a hukuncin dauri na shekaru 2 a kasar Faransa

Wani malamin akidar Shi'a kuma haifaffen kasar Iran ya yankar wa kansa tikitin zama a gidan Dan Kande yayin da wata kotun kasar Faransa ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru biyu bayan sabawa hukumar shige da fice.

Kotun kasar Faransa ta yanke wa malam Muhammad Baraeikechi Ghaleshi hukuncin zaman gidan sarka na tsawon shekaru biyu bayan ta same shi da laifin taimakawaa 'yan ci-rani ketarewa zuwa kasar Ingila ta hanyar kananan jiragen ruwa.

Kazalika kotun ta yankewa wani abokin tarayyar malamin da su ke aikata wannan mummunan harka hukuncin dauri na zama a gidan kaso duk da cewar wa'adin bai kai wanda malamin zai shafe ba wajen bai wa duga-dugan sa hutu.

Bayan gudanar da bincike da sanya idanun lura kan malam Ghaleshi na tsawon watanni kimanin hudu, hukumomin tsaro sun damke shi tare da abokin huldar sa ta aikata wannan babban laifi mai yiwa kowace kasa zagon kasa.

KARANTA KUMA: Bikin Sallah: Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 2, Mutane 8 sun jikkata a jihar Ogun

Malam Ghaleshi mai shekaru 39 a duniyar kuma malamin akidar Shi'a a birnin Rouen na kasar Faransa ya shiga hannu tare da abokin huldar sa a watan Afrilun da ya gabata bayan kama su da laifin taimakawa 'yan ci-rani masu fafutikar ketarewa zuwa kasar Ingila daga Faransa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel