Dan Najeriya ya yi rabon kayan tallafi ga al'umma a masallacin Makkah

Dan Najeriya ya yi rabon kayan tallafi ga al'umma a masallacin Makkah

Fitaccen mai karatun Kur'ani a Najeriya Sheikh Nurudeen Umar Tahir kuma Direktan Makarantar Nurut Tilawah da ke Zaria yana daya daga cikin mutanen da mahukunta a kasar Saudiyya da ke kula da walwalan mahajjata da masu Umrah suka zaba domin rabon kayayakin sallar ga al'umma a masallacin Makkah da ke Saudiyya.

An yi rabon kayayakin ne a ranar Talata 4 ga watan Yuni karkashin jagorancin Sheikh Adil da kuma Shugaban sashin kulawa da dakin karatu na masallacin Makkah, Sheikh Gazzi Bin Fahad.

A yayin hirar da akayi da shi kan muhimman nauyin da aka daura masa, Sheikh Tahir ya ce: "Wannan muhimmiyar dama ce domin yana da wahala ka ga an bawa bakar fata dan Afirka irin wannan aiki, muna matukar godiya da aka bamu damar yin wannan aikin mai dimbin lada da kuma daga darajar Najeriya da 'yan Najeriya."

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

A farkon 2019, babban malamin addinin ya jagoranci wata tawaga daga Nurut Tilawah zuwa Saudiyya inda suka ziyarci wurare masu yawa ciki har da ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudiyya inda aka yi addu'o'in samun zaman lafiya da daukaka ga Najeriya.

Duk dai cikin bukukuwan Sallah, Legit.ng ta ruwaito cewa wasu mabiya adidnin Kirista a Habasha sun hada hannu da musulmi wurin sharar filin motsa jiki gabanin sallar Idi.

Frai Ministan kasar Abiy Ahmed yana daya daga cikin wadanda aka hango suna sharar filin da za a gudanar da Sallar Idi a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel