Bikin Sallah: Buratai ya ziyarci sojoji da ke gwagwarmaya a fagen fama

Bikin Sallah: Buratai ya ziyarci sojoji da ke gwagwarmaya a fagen fama

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ziyarci dakarun Sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji a hedkwatan su Gusau a jihar Zamfara domin kara musu kwarin gwiwa.

Kakakin rundunar soji, Kwanel Sagir Musa ya ce Buratai ya kai ziyarar ne domin taya sojojin da ke fafatawa da masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga murnar Sallah wato Eid El Fitr.

Musa ya yi bayanin cewa shugaban hafsoshin sojojin ya samu wakilcin shugaban sashin bayar da horo a hedkwatan soji, Manjo Janar Lamidi Adeosun.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Kwanel Musa ya ce: "Shugaban hafsoshin sojojin Najeriya da ya samu wakilcin shugaban sashin bayar da horo a hedkwatan soji, Manjo Janar Lamidi Adeosun ya yi sallar Eid tare da dakarun sojoji a hedkwatan Operation Sharan Daji da ke Gusau a jihar Zamfara.

"Manjo Janar Lamidi Adeosun ya yi jawabin fatan alheri na hafsin hafsoshin sojojin Najeriya, Lt Janar TY Buratai ga dakarun sojojin na 1 Brigade da Hadarin Daji jim kadan bayan kammala sallar Eid.

"Ya yabawa sojojin bisa sadaukarwa da hidima da jajircewa wurin kare kasarsu.

"Ya bukaci su cigaba da dagewa a wurin kawo karshen ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga da sauran kallubalen tsaro da ake fama da shi a Najeriya.

"Babban limamin 1 Brigade, Capt A Kado ya yi addu'ar zaman lafiya da samun tsaro a Najeriya. An kuma yi addu'a ga wadanda suka rasa rayyukansu wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar mu.

"Bayan kammala addu'o'in, Manjo Adeosun da tawagarsa sun ziyarci sansanin soji da ke Kauran Namoda inda nan ma ya isar da sakon fatan alheri na babban hafsan sojin kasa na Najeriya ga sojoji da sauran hukumomin tsaro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel