Ba dolene sai mata sun sanya Hijabi a Saudiyya ba - Yarima Salman

Ba dolene sai mata sun sanya Hijabi a Saudiyya ba - Yarima Salman

Tun lokacin da aka bayyana Mohammad bin Salman a matsayin Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, yaci alwashin mayar da kasar ta zama abar kwatance a yankin gabas ta tsakiya

Idan ba a manta ba a ranar 24 ga watan Yuni, 2018 Yariman ya saka an kyale mata suna tukin mota a kasar ta Saudiyya, inda a shekarun baya hakan ba karamin laifi bane a kundin tsarin kasar.

Yanzu kuma da canje-canje ke samun gurin zama a kasar ta Saudiyya, Yarima mai jiran gado Mohammad bin Salman ya kara taso da wata bukatar tashi, a lokacin da yayi hira da manema labarai a gidan talabijin na CBS dake kasar ta Saudiyya.

Ba dolene sai mata sun sanya Hijabi a Saudiyya ba - Yarima Salman
Ba dolene sai mata sun sanya Hijabi a Saudiyya ba - Yarima Salman
Source: Facebook

A bayanin da Yariman yayi, ya bayyana cewa ba dole bane mata su dinga sanya Hijabi a kasar. Hijabi wani kaya ne da matan musulmai na zamanin da suke amfani dashi domin rufe jikinsu.

Ya ce mata yanzu suna da zabi na kayan da zasu sanya a kasar, ba dole bane sai sun saka Hijabi, zasu iya amfani da kowane irin kaya mutukar zai rufe jikinsu.

KU KARANTA: Wani boka ya bayyana wahayin da aka yi masa akan nasarar Atiku Abubakar a kotu

Yariman ya bayyana cewa addinin Musulunci ya bayyana cewa mata su sanya kaya wadanda zasu rufe jikinsu kamar yadda aka hukunta akan maza, amma babu inda aka ce dole sai mace ta sanya Hijabi.

Ya ce hukunci ya rage ga matan wurin zabar kayan da zasu sanya, amma daga yanzu babu wannan dokar a kasar.

Maganganun nashi sun biyo bayan alwashin da ya ci na cewa zai canja kasar ta Saudiyya ta zama tamkar Turai a yankin gabas ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel