An kama Yariman Saudiyya na boge kan damfara

An kama Yariman Saudiyya na boge kan damfara

Wani mutum mai suna Anthony Gignac da ke ayyana kansa a matsayin Yariman Saudiyya ya shiga hannun 'yan sanda kuma sun mika shi gaban kotu domin a yi masa shari'a.

Babbar mai shari'a ta Amurka, Fajardo Orshan ta ce Anthony Gignac ya kwashe tsawon shekaru 30 yana damfarar mutane a fadin duniya da sunan wai shi yariman Saudiyya ne.

Kazalika, wani alkali a jihar Florida ya ce Gignac mai shekaru 48 da haihuwa dan damfara ne da ya yi rayuwa a matsayin dan masarautar Saudiyya kamar yadda Bbc ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Kotu ta yanke wa Yariman na boge daurin shekaru 18 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin zamba cikin aminci.

Kotun ta ce an kama Gignac sau 11 a cikin shekaru 30 da suka gabata sakamakon 'damfara da sunan Yarima.'

Gignac ya rika saka gwala-gwalai da wasu kayayakin alatu a shafukan sada zumunta da sunan yana balaguro cikin jiragen sama da motoci na alfarma dauke da lambobin diflomasiyya.

Binciken da aka gudanar ya nuna ya yi damfarar da ta kai dalar Amurka miliyan 8.

Gignac yana kuma sanya tufafi gargajiya irin na Saudiyya tare da agogunan hannu masu matukar tsadan gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel