Bikin Sallah: Hotunan ziyarar da Osinbajo da wasu jiga-jigan gwamnati suka kai wa Buhari

Bikin Sallah: Hotunan ziyarar da Osinbajo da wasu jiga-jigan gwamnati suka kai wa Buhari

Shugaban Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin mataimakinsa, Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da famanan sakatare na Abuja, Chinyeaka Ohaa da Philip Aduda yayin da suka kai masa ziyarar murnar bikin sallah karama.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da halayyar da suka kasance akai cikin watan Ramadana.

Ya kuma nuna farin cikinsa bisa gudanar da zabe da akayi a kasar cikin kwanciyar hankali da lumuna, duk da cewa anyita hasashen za’a samu tashin hankali lokacin zaben.

Yawon Sallah: Osinbajo da wasu jiga-jigan gwamnati sun kaiwa Buhari ziyara

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo da wasu yara yayin da suka kai wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara a ranar Sallah
Source: Twitter

Yawon Sallah: Osinbajo da wasu jiga-jigan gwamnati sun kaiwa Buhari ziyara

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da Chinyeaka Ohaa da wasu manyan baki yayin ziyarar Sallah ta suka kai wa shugba Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Yawon Sallah: Osinbajo da wasu jiga-jigan gwamnati sun kaiwa Buhari ziyara

Mataimakin shugaban kasa Yemu Osinbajo da shugaba Muhamadu Buhari da Chinyeaka Ohaa yayin ziyarar sallah da suka kai fadar shugaban kasa
Source: Twitter

Yawon Sallah: Osinbajo da wasu jiga-jigan gwamnati sun kaiwa Buhari ziyara

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa yayin ziyarar bikin sallah karama a Abuja
Source: Twitter

A sakonsa na goron sallah shugaba Buhari ya yabawa hukumar zabe bisa kokarinta na shirya zabe mai inganci a kasar nan. Kana kuma ya jinjinama ‘yan Najeriya a kan juriya da kuma nuna amincewarsu ga da abinda ake kira dimokuradiyya.

“Kafin zaben 2019 wasu tsirarun mutane sun yita cece kuce kan cewa wannan zabe zai zo da tangarda. Sai ga shi duk da maganganunsu anyi zabe lafiya ba tare da wata fitina ba. Duk wadannan zantukan nasu babu ko guda da yayi tasiri a lokacin zaben saboda anyi komi cikin lumana da kwanciyar hankali.

“Bari inyi amfani da wannan damar na tunatar da ‘yan Najeriya sadaukar min da kuri’arku da ku kayi ba zai tafi a banza ba. Ina mai tabbatar muku da cewa za kuyi na’am da wannan gwamnatin ta wa.” Inji Buhari kamar yadda hadiminsa Garba Shehu ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel