Wani boka ya bayyana wahayin da aka yi masa akan nasarar Atiku Abubakar a kotu

Wani boka ya bayyana wahayin da aka yi masa akan nasarar Atiku Abubakar a kotu

- Akwai yiwuwar dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar zai yi nasara a kotu, idan har hasashen wani boka ya zamanto gaskiya

- Igwe Onyeachonam Ofomba yayi hasashen cewa anyi masa wahayin dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar zai zama shugaban kasar Najeriya

- Ya ce idan har kotu bata bayyana Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Najeriya ba, zai daina aikin bokancin sa.

Wani boka a jihar Anambra, mai suna Igwe Onyeachonam Ofomba, yayi hasashen cewa anyi masa wahayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai zama shugaban kasar Najeriya a wannan shekarar.

Ofomba ya ce Atiku Abubakar zai samu nasara a karar da ya shigar zuwa kotun daukaka kara a Abuja, inda ya bayyana cewa idan har kotu bata bai wa Atiku kujerar shugabancin kasar nan ba zai daina bokanci.

KU KARANTA: Ganduje yayi belin fursunoni dari biyu daga gidan yari

Jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa Ofomba ya bayyana hakan ne a gurin wani bikin da aka gabatar a karamar hukumar Anambra ta gabas.

Ya bayyana cewa anyi mishi wahayin cewa Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya a wannan shekarar, inda ya bayyana cewa babu abinda zai hana tsohon mataimakin shugaban kasar zama shugaban kasa a wannan shekarar.

Hakazalika, wani na hannun daman Atiku, Comrade Timi Frank ya bayyana cewar akwai nasara duk da cewar an rantsar da shugaban kasar a karo na biyu.

Ya ce magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar zasu jira har lokacin da kotun koli zata bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel