Bikin Sallah: Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 2, Mutane 8 sun jikkata a jihar Ogun

Bikin Sallah: Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 2, Mutane 8 sun jikkata a jihar Ogun

Tabbas mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya yayin aukuwar wasu hadurra biyu daban daban a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan cikin birnin Abeokuta na jihar Ogun a ranar Talata ta bikin karamar Sallah.

Kwamandan hukumar kula da manyan tituna reshen jihar Ogun, Mista Clement Oladele, shi ne ya bayar da shaidar tabbacin wannan mummunan lamari cikin wata sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Laraba.

Oladele ya ce hatsarin farko ya auku da misalin karfe 4.52 na safiyar Talata a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan daura da gidan man fetur na AP a garin Shagamu.

A yayin da aukuwar hatsarin na biyu da ya maimatu akan wannan hanya ta wakana da misalin karfe 3.54 na Yammacin Talata, rayukan Mutane biyu sun salwanta yayin da mutane takwas suka jikkata.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Idera dake garin Shagamu yayin da aka killace gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya a asibitin koyarwa na jami'ar Olabisi Onabanjo.

KARANTA KUMA: Shugaban hafsin sojin kasa ya hori dakaru akan faduwar gaba

Hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi ta FRSC na ci gaba da gargadin masu ababen hawa da suka tabbatar da kiyaye ka'idojin tuki yayin gudanar safarar su musamman a wannan lokuta na shagulgulan Sallah.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel