Shugaban hafsin sojin kasa ya hori dakaru akan faduwar gaba

Shugaban hafsin sojin kasa ya hori dakaru akan faduwar gaba

A ranar Talatar da ta gabata shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya kaiwa dakaru ziyara a sansanin Hadarin Daji da ke birnin Gusau na jihar Zamfara domin kara masu karsashi da kuma kwarin gwiwa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ziyarar Buratai na zuwa ne a daidai ranar da shugaban hafsin sojin sama na Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya hori dakaru akan tabbatar da ganin karshen duk wasu masu tayar da zaune tsaye a fadin Najeriya.

A cewar kakakin rundunar sojin kasan Najeriya, Kanal Sagir Musa, Buratai ya yi tattaki zuwa jihar Zamfara domin taya dakaru murnar bikin karamar Sallah yayin da suke filin daga na yakar 'yan baranda da masu garkuwa da mutane.

Cikin sanarwar da Kanal Musa ya bayar da shaida, Manjo Janar Lamidi Adeosun ne ya wakilci shugaban hafsin sojin kasan Najeriya wajen kai wannan ziyara. Manjo Janar Lamidi ya hori dakaru akan kawar da faduwar gaba da zukatan su a yayin kare martabar kasar nan.

KARANTA KUMA: Oshiomhole da Oyegun sun zargi juna kan faduwar jam'iyyar APC a jihohi 5 na Najeriya

Kazalika babban jami'in sojin tare da tawagar sa sun kai ziyara sansanin dakaru a karamar hukumar Kauran Namoda inda ya isar masu da sakon Buratai na taya murnar Sallah da kuma gargadin su a kan karsashi da kwarin gwiwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel