An kama wani matashi da ke kai wa Boko Haram kayayyaki hada bama-bamai a Borno

An kama wani matashi da ke kai wa Boko Haram kayayyaki hada bama-bamai a Borno

Jami’an tsaro na Civil Defence a Borno a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, sun tabbatar da kama wani Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 wanda ake zargin shi kaiwa yan ta’addan Boko Haram kayayyakin hada bama-bamai a Maiduguri.

Kwamandan rundunar, Ibrahim Abdullahi ya bayyana hakan a hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Abdullahi ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kama mai laifin ne a ranar 25 ga watan Afrilu, biyo bayan wani rahoton kwararru da suka samu yayinda yake a hanyarsa ta kai wa yan ta’addan Boko Haram kayayyakin bam.

Ya bayyana cewa binciken farko da hukumar ta gudanar, ya nuna cewa mai laifin na kai way an ta’addan baturan waya, agogunan hannu da kuma kwamfuta da suke amfani dasu wajen dana bama-bamai don hallaka al’umma.

“Mai laifin wanda ke badda kammani a matsayin mai adaidaita sahu a cikin gari, ya aiwatar wa yan ta’addan ayyuka da dama.

KU KARANTA KUMA: Guru Maharaji ya bukaci Buhari ya nada shi a matsayin mai bashi shawara domin ya jagoranci ma’aikatar man fetur da sauransu

“Yana kuma da asusun bankuna daban-daban, inda yake samun kudade daga Boko Haram a watanni shida da suka gabata.

“Ya kan samu makudan kudade daga kasar Chadi, ta hanyar wani da ke tsakani," Inji shi.

Kwamnadan ya jadadda cewa Mohammed da abokan aikinsa sun taka rawar gani sosai wajen kaddamar da hare-hare da dama a cibiyoyin bauta da kasuwanni a Maiduguri da kewayenta.

Abdullahi ya kuma jadadda jajircewar hukumar wajen taimakawa kokarin sojoji, yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen magance ta’addanci a arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel