Ganduje yayi belin fursunoni dari biyu daga gidan yari

Ganduje yayi belin fursunoni dari biyu daga gidan yari

- Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ceto fursunoni dari biyu daga gidan yari

- Gwamnan ya bukaci fursunonin su zamanto masu halaye na gari, sannan su taimaka gurin kawo cigaba ga al'umma

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi belin 'yan gidan yari guda 200 da kimanin kudi naira miliyan 11.

Ganduje wanda ya kai ziyarar sallah gidan yarin Goron-Dutse, ya bayyana cewa an kawo mishi kimanin mutane 2,517 wadanda aka kama a cikin shekaru hudu da yayi akan mulki.

Ganduje ya bayyana cewa, "Mun yi belin su, bayan bin dukkanin dokokin da suka kamata. Sannan muna yin hakan domin bin umarnin da aka bai wa gwamnoni wurin belin 'yan gidan yari domin rage cunkoso a gidajen yari."

KU KARANTA: Za a kasafta kudaden marigayi Janar Sani Abacha tsakanin kasashe uku

Hanyoyin da muka bi wurin fito d 'yan gidan yarin sun hada da, wadanda suka kasa biyan kudin belin dinsu, da kuma wadanda basu da laafiya, da tsofaffi.

Ganduje ya shawarci wadanda aka saki din akan su zamanto masu halaye na gari, sannan su zage wurin kawo gyare-gyare a wuraren da suke zaune.

Gwamnan jihar dai yana ta kokarin yin ayyukan alkhairi tun bayan rantsar dashi da aka yi a matsayin gwamnan jihar karo na biyu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel