Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Rundunar 'Yan sandan Jihar Niger ta kama wani mutum mai shekaru 21, Umar Audu da ake zargi da kashe wani Abubakar Muhammadu mazaunin rugar fulani da ke kauyen Wawa a New-Bussa a karamar hukumar Borgu na Jihar Niger.

'Yan sandan sun tabbatar da kama wanda ake zargin a ranar Talata inda suka ce tawagar 'yan sanda da ke New-Bussa ne suka kama shi bisa zargin kashe Muhammadu.

Ana zargin ya kashe marigayin wanda su ke zaune a ruga daya ne saboda yana zargin sa da neman matarsa da lalata.

Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa

Magidanci ya kashe makwabcinsa saboda zarginsa da neman matarsa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun tafka ma 'yan Boko Haram mummunan asara a Abaganaram

An gano cewa a cikin watan Mayun 2019, matar wadda ake zargin Hassana Audu tayi karar marigayin wurin mijinta cewa yana nemanta amma ba ta bashi hadin kai ba.

Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya yi wa marigayin gargadin ya nesanta kansa da matarsa amma bai dena ba.

A ranar abin ya faru, wanda ake zargin ya fusata sosai kuma ya dauki doka a hannunsa inda ya kai wa marigayin hari da adda ya sare shi a kai wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar Muhammadu.

A hirar da Northern City News tayi da wanda ake zargin ya ce, "Ban yi nadamar kashe shi ba saboda Muhammadu ya zabi ya mutu kamar kaza. Ba zai sake neman matan aure ba a wani rayuwar.

"Na shirya wa duk wani hukunci da doka ta tanada min. Buri na ya cika saboda Muhammadu ba zai sake ganin mata ta ba. Allah zai masa hisabi."

Kakakin 'yan sandan jihar, Muhammadu Abubakar ya ce za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu idan an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel