Oshiomhole da Oyegun sun zargi juna kan faduwar jam'iyyar APC a jihohi 5 na Najeriya

Oshiomhole da Oyegun sun zargi juna kan faduwar jam'iyyar APC a jihohi 5 na Najeriya

Biyo bayan shan mugunyar kaye na jam'iyyar APC a wasu jihohin biyar na Najeriya a kakar babban zaben kasa da kuma bayan sa, ana ci gaba da zargin juna tsakanin tsohon shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun da kuma magajin sa.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole, a ranar Talatar da gabata ta ya ce jam'iyyar adawa ta PDP ta yi galaba a kan su cikin wasu jihohin kasar nan a sakamakon rashin kafa tubalin ladabi da kuma da'a da tsohon shugaban jam'iyyar ya haifar.

Kwamared Oshiomhole ya ce rashin assassa ingataccen tubali na jagoranci a karkashin gudanarwar Cif Oyegun ya sanya jam'iyyar APC ta susuce wajen shan mugunyar kaye a hannun jam'iyyar adawa ta PDP cikin wasu jihohi biyar na kasar nan.

Cikin na sa martanin tsohon shugaban jam'iyyar ta hanyar mai bashi shawara a kan hulda da al'umma, Cif Ray Morphy ya ce Oshiomhole ya dimauce wajen neman wanda zai yiwa zargi akan nakasun da jam'iyyar ta samu a yayin da yake jagorancin ta.

KARANTA KUMA: Buhari bai amince da samar da 'yan sandan jiha ba - Fadar Shugaban kasa

A wani bangaren kuma, kakakin jam'iyyar APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, cikin wata hirar sa da manema labarai a ranar Talata ya ce faduwar jam'iyyar su a jihohin Oyo, Imo, Bauchi, Adamawa da kuma Zamfara ta bayu ne a bisa dalilai masu sabani da juna ta fuskar madogara.

Mallam Lanre ya ce babu rashin samun goyo bayan al'umma ta fuska kuri'u cikin jerin jihohi biyar da jam'iyyar APC ta sha kasa a hannun jam'iyyar adawa ta PDP illa iyaka dalilai mabambanta juna da suke da alaka da jagoranci a jihohin.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel