Duk kai ne ka haddasa matsalolin da mu ke fuskanta - APC ta mayar wa Oyegun martani

Duk kai ne ka haddasa matsalolin da mu ke fuskanta - APC ta mayar wa Oyegun martani

Jam'iyyar APC mai mulki ta ce tsohon shugabanta na kasa, Cif Odigie Oyegun, ya daure wa rashin da'a gindi lokacin da yake jagorancin al'amuran jam'iyyar.

Mallam Lanre Issa-Onilu, sakataren yada labaran jam'iyyar APC, a wata ganawar sa da manema labarai, ya ce kwamitin gudanarwa na jam'iyyar karkashin jagoranci Oyegun ya gaza hukunta wasu tsirarun manyan 'yan siyasa da suka ki bin dokoki da tsare-tsaren jam'iyya.

Oyegun ya bayyana cewar Oshiomhole bashi da hakurin da zan iya jagorantar jam'iyyar siyasa. Da ya ke magana a kan Oshiomhole, toshon shugaban jam'iyyar ya ce, "da bakinsa ya ke fara aiki kafin ya yi aiki da tunaninsa, hakan ne ya sa koda yaushe ya ke a cikin bata wa da mambobin jam'iyya."

Da yake mayar da martani a kan sukar da Oyegun ya yi wa Oshiomhole, Issa-Onilu ya ce gazawar Oyegun wajen daukar matakan a kan ladabtarwa a kan mambobin jam'iyya ne ya jawo dukkan matsalolin da APC ke fuskanta musamman daga bangaren mambobinta na majalisun tarayya.

"Dole a samu matsala, a kusa ko a nesa, idan ya kasance jam'iyya ko wata hukuma ko kuma kungiya ta kasa amfani da dokokinta domin sarrafa mambobinta

"Ba abin kunya bane mu shaida wa duniya cewar shugabancin jam'iyyar mu a karkashin Oyegun ya gaza tunkarar wasu tsirarun manyan mambobin jam'iyya da suka girmama dokoki da tsare-tsaren jam'iyya," a cewar Issa-Onilu.

Dangane da asarar kujerun da APC ta yi a zabukan da a kammala a cikin shekarar nan, Issa-Onilu, ya ce ko kadan babu laifin shugabanci jam'iyya, laifin na wadanda aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar ne kuma suka gaza fita kunyar jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel