Buhari zai cika alkawaran da ya daukar ma yan Najeriya – IBB ya bayar da tabbaci

Buhari zai cika alkawaran da ya daukar ma yan Najeriya – IBB ya bayar da tabbaci

Tsohon Shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), ya nuna karfin gwiwa akan kokarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na magance matsalolin tsaro da yayi wa kasar katutu.

Da yake magana da manema labarai a gidansa na hilltop da ke Minna a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, tsohon Shugaban kasar yace Buhari na da karfin magance matsalolin, yayinda ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri da Shugaban kasar.

A cewarsa, Buhari mutum ne da aka sani mai magana daya.

Ya bayyana cewa shugaba Buhari ya sha jadadda jajircewar gwamnatinsa don kawo karshen ta’addanci a arewa maso gabas da sauran matsalolin tsaro da ke addabar fadin kasar a mulkinsa na biyu.

IBB yace yan Najeriya su riki Buhari da kalamansa, inda ya kara da cewa matsalar rashin tsaro wani lamari ne mara dorewa wanda za a shawo kansa nan da dan wani lokaci kadan.

Ya kuma nuna karfin gwiwa akan kokarin Shugaban kasar na kai kasar matakin ci gaba da bunkasa.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da matar da ta hada kai da wasu mutane wajen garkuwa da mijinta

Babangida yace abunda ake bukata a yanzu shine yan Najeriya su mara wa Shugaban kasar baya domin cimma nasara a ayyukan da ke gabansa.

Ya kuma bukaci yan Najeriya da su yi watsi da duk abunda zai kawo wariya, cewa zaman lafiya da hadin kai shine ci gaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel