Tirkashi: An gano wasu makudan miliyoyin da Abacha ya boye a Amurka

Tirkashi: An gano wasu makudan miliyoyin da Abacha ya boye a Amurka

Wasu makudan miliyoyi da suka kai akalla Fam miliyan 200, mallakan tsohon shugaban kasan mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, sun bayyana a bankin Jersey da ke kasar Amurka

Janar Sani Abacha, wanda ya shugabanci Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998, ya boye wasu kudade ta hanyar bankin kasar Amurka.

An boye kudin ne a wani asusun banki dake Jersey na kamfanin Doraville Properties Corporation.

A yanzu haka, gwamnatin kasar ta rike kudin har sai lokacin da kasar Amurka da Najeriya sun tattauna da yarjejeniya kan yadda za'a dawo da kudin.

A bangare guda, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewar za ta fara kashe kudaden da ta kwato daga cikin arzikin da tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya kai su kasashen waje daga watan gobe na Yuli.

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnati ta ce zata kashe kudaden ne ta hanyar yi ma yan kasa hidima, kamar yadda mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tallafa ma jama’a, Maryam Uwais ta bayyana a ranar Alhamis,28 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel