Majalisa: Takarar Gbajabiamila ta fara fuskantar tarnaki sakamakon wata kara da aka shigar da shi

Majalisa: Takarar Gbajabiamila ta fara fuskantar tarnaki sakamakon wata kara da aka shigar da shi

Jastis Inyang Ekwo, alkalin wata babbar kotun gwamnatin tarayya, ya amince da aika wa dan takarar neman shugabancin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, takardar sammaci ta hannun lauyansa, Olasupo Azeez.

An shigar da karar neman haramta wa Gbajabiamila zama mamba a majalisar wakilai a gaban kotun bisa dogaro da wani laifi mai nasaba da zamba da ya taba aikata wa lokacin da yake aikin lauya a kasar Amurka.

Jastis Ekwo ya ce aika sammaci ta hannun lauyan ya zama tilas ne saboda kotun ta gaza mika sammacin zuwa ga Gbajabiamila hannu da hannu.

"Irin wannan kara na jan hankalin jama'a, a saboda haka dole ka kasance cikin shiri," alkalin ya fada wa Azeez.

Sakamakon haka, Jastis Ekwo ya daga sauraron zuwa ranar Juma'a, 7 ga watan Yuni.

Wani mutum mai suna Philiph Undie ne ya shigar da karar Gbajabiamila ta hannun lauyansa, Barista Ayodele Justice. Ya shaida wa kotun cewar Gbajabiamila bai cancanci zama mamba a majalisar wakilai ba saboda an taba gurfanar da shi a wata kotun kasar Amurka da laifin zambar kudi $25,000.

Majalisa: Takarar Gbajabiamila ta fara fuskantar tarnaki sakamakon wata kara da aka shigar da shi

Femi Gbajabiamila
Source: UGC

A cewar Undie, kasar Amurka ta kwace lasisin aikin lauya na Gbajabiamila tare da dakatar da shi tsawon watanni 36 shekara uku).

DUBA WANNAN: Buhari ya soki masu yiwa talakan Najeriya bukulu

Andie ya ce Gbajabiamila, lokacin yana amfani da sunan Femi Gbaja, ya taba karbar kudin diyyar da aka biya wani mutum da ya kare a kotu amma maimakon ya bawa mutumin kudinsa sai ya zuba su a asusun bankinsa.

A cewar Andie, halin da Gbajabiamila ya nuna ya ci karo da manufar gwamnatin jam'iyyar APC na yaki da cin hanci da rashawa.

Hatta gamayyar kungiyar jam'iyyun siyasar Najeriya (CUPPS) ta yi kira a kan a haramta wa Gabajabiamila saboda, a cewarsu, akwai alamomin tambaya a tattare da kimarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel