Mafi karancin albashi :Gwamnati ba zata iya cutan ma’aikata ba, inji kungiyar kwadago

Mafi karancin albashi :Gwamnati ba zata iya cutan ma’aikata ba, inji kungiyar kwadago

-Kungiyar kwadago ta ce tana kyautata zaton cewa gwamnatin tarayya zata cika masu alkawarin kaddamar da mafi karancin albashin N30,000.

-Shugaban TUC, Bobboi Kaigama ne ya bada wannan tabbacin a wurin wani taro na musamman da ya halartar a Akure babban birnin jihar Ondo inda yake cewa maganar mafi karancin albashin sam babu cuta a cikinta.

Kungiyar kwadago ta TUC ta tabbatar wa ma’aikata cewa ya zama dole gwamnatin tarayya ta kaddamar da mafi karancin albashin N30,000.

Shugaban kungiyar TUC, Bobboi Kaigama ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Akure babban birnin jihar Ondo yayin wani taro na musamman da kungiyarsa ta shirya.

KARANTA WANNAN:Rikicin APC: Oyegun ya zunguri Oshiomole da wata babbar magana

Yace sam mafi karancin albashi ba maganar yaudara bace. Shugaban wanda sakataren kungiyar ya wakilta Musa Lawal yace shugaban kasa ya fitar da kwamitin kwararru akan duba lamarin mafi karancin albashin domin a kaddamar dashi.

Shugaban TUC ya shaidawa ma’aikata cewa suna bin abin domin ganin yadda lamarin zai kaya. Bukatarsu itace kada ya kasance an samu tangarda ko kadan.

“ Sam ba bacci mukeyi ba, muna nan tsaye kan kafafunmu. Fada kan mafi karancin albashi yanzu muka fara, ba kuma zamu gajiya ba sai hakar mu ta cinma ruwa.” Inji Kaigama

“ Bamu taba yarda cewa gwamnati na iya yaudarar ma’aikatanta ba. Saboda ni na damu kwarai kan walwalar ma’aikata na kuma na yadda da shugaba Buhari kan cewa bai taba cin amana ba.” A cewarsa.

Idan baku manta ba shugaban kasa ya sanya hannu kan takardar mafi karancin albashin ne a watan Afrilun da ya gabata.

Bayan kungiyar ta kammala taro sun sake gudanar da zaben sabbin shugabannin kungiyar reshen jihar ta Ondo. Zababbun shugabannin sun fara ne daga kan babban jigon kungiyar har zuwa kan masu kananan mukamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel