Rikicin APC: Oyegun ya zunguri Oshiomole da wata babbar magana

Rikicin APC: Oyegun ya zunguri Oshiomole da wata babbar magana

-Dangantaka tayi tsami a tsakanin Oshiomole da tsohon shugaban jam'iyar ta APC Cif John Odigie Oyegun inda ake ta musayar maganganu.

-Oyegun yace da Oshiomole ya cire girman kai yazo a baje masa hanyoyin samun nasara domin ciyar da jam'iya gaba.

Tsohon shugaban jam’iyar All Progressives Congress APC Cif John Odigie Oyegun ya sokawa Kwamarad Adams Oshiomole magana inda yake cewa shugaban jam’iyar APC laifin wasu yake hangowa ba tare da yana duba nasa ba.

“ Kada Oshiomole ya rushe abinda wasu suka gina. Idan yana bukatar a karantar dashi yadda zai tafiyar da jam’iyar ya zo ya nemi taimako, a shirye nake da in taimaka mashi.” Inji tsohon shugaban.

KU KARANTA:Yau take sallah: Sakon Shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya

Cif Oyegun yayi wannan maganar ne a matsayin martini ga sakaraten hulda da jama’a na jam’iyar ta APC a yanzu wato Mallam Lanre Issa Onilu wanda ya bayyana tsohon shugaban jam’iyar a matsayin maras tsari wanda ya mayar da jam’iyarsu tamkar PDP.

Shi kuwa hadimin Cif Oyegun, mai kula hulda da jama’a Ray Morphy a nashi zancen da ya fitar kan lamarin cewa yayi jagorancin maigidansa daya ne tamkar da goma a wurin jam’iyar APC.

Abinda takardar ta kunsa ya hada da, rashin samun zaben fidda gwani mai inganci da haryanzu wasu yan takarar ke kotu domin warwarware matsalarsu. A karkashin jagorancin Oshiomole wanda ya kai kimanin shekara daya kenan a yanzu inda da dama daga cikin yan jam’iyar APC ke ta sauya sheka.

“Kazalika, lokacin da Oyegun yayi jagoranci abin ba haka ya kasance ba. An samu hadin kai da kuma zaman tsintsiya madaurinki daya tare da samu nasori masu yawan gaske.” Inji hadimin Oyegun.

Oshiomole a matsayinsa na babba bai iya magance karamar matsala dake damun jam’iyar hakan ne ya janyo APC ta rasa jihohi da dama duk da tarin karfin da take dashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel