Bikin sallah: Yan sanda 2000 aka baza jihar Nasarawa domin samar da tsaro

Bikin sallah: Yan sanda 2000 aka baza jihar Nasarawa domin samar da tsaro

-Kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa ya bada tabbaci ga yan jarida cewar babu fargaba a fannin tsaro a jihar saboda akwai jami'an yan sanda cike a muhimman wurrare na jihar.

-Bola Longe ya sake yin kira tare da bada lambobin salula don gudun karta kwana ga jama'ar jihar ta yadda da sun ga wani abu na daban za su iya kiran lambobin.

Kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa Bola Longe yace rundunarsa ta baza yan sanda 2000 a jihar Nasarawa domin samar da tsaro a lokacin gudanar da bikin karamar sallah a fadin jihar.

Kwamishinan ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, “ Rundunar mu ta shirya tsaf domin samar da tsaro na musamman lokacin gudanar da bukukuwan sallah a jihar Nasarawa. Wasu daga cikin jami’an mu za su sanya farin kaya domin leken sirri cikin jama’ar gari a lungu da sako.

KU KARANTA:Yau take sallah: Sakon Shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya

Yayin da sauran kuwa za su rika yin kai kawo a kan manya tituna Nasarawa domin tabbatar da komi ya tafi kan tsari ba tare da rikici ba musamman ga matafiya.”

A cewarsa, mun riga da mun tura jami’an mu a duk wuraren sallar idi da kuma sauran wuraren shakatawa domin samar da yin bukukuwan cikin lumana.

Kwamishinan yayi kira jama’ar garin na su kasance masu bin doka da oda kamar yadda suka saba. Sa’anan kuma ya bada lambobin salula saboda ko ta kwana, ga lambobin kamar haka: 08108795930 and 08112692680.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel