Dalilin zuwan Buhari taron OIC da kuma abinda ya samo wa Najeriya, inji hadiminsa

Dalilin zuwan Buhari taron OIC da kuma abinda ya samo wa Najeriya, inji hadiminsa

-Garba Shehu yayi bayani dalla-dalla akan halartar taron OIC da shugaban kasa inda ya ke cewa hakika tafiyar na da muhimmanci kwarai da gaske ga Najeriya.

-Wannan martanin nasa ya biyo bayan ce-ce kuce da jama'a ke tayi ne kan cewa sam bai dace shugaban kasa ya halarci wannan taron ba kasancewar kwana daya ne tsakaninsa da ranar da aka rantsar da shi a karo na biyu.

Hadimin shugaban kasa, Garba Shehu wanda yake bashi taimako na musamman akan harkokin yada labarai ya tanka kan ce-ce kuce da ake tayi kan tafiyar shugaba Muhammadu Buhari da yayi zuwa kasar Saudiya domin halartar taron OIC.

Yan Najeriya da dama na ganin bai kamata shugaban kasa yayi wannan tafiya ba kasancewar ta zo bayan kwana daya tak da rantsar da shi a zangonsa na biyu.

KU KARANTA:Yau take sallah: Sakon Shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya

Shi kuwa Garba Shehu bai ga laifin maigidansa ba kan wannan tafiya inda yake cewa “ shugaba yayi abinda ya dace da kudurin kasa ne yayin da yayi biris da yan kushe.”

“Cikin martaninsa hadimin ya nuna mana cewa shugaba Buhari wanda shine jagoran kasashen Afrika 16 dake kungiyar yayi jawabi mai ma’ana a wurin taron.

"Bugu da kari shi ne shugaban kasa na uku daga Najeriya wanda ya yi jawabi wurin taron OIC. Hakika shugaba ya yi manganganu masu matukar amfanin gaske duba ga cewa yana wakiltar nahiyar Afrika baki dayanta.

"Abu na farko shine matsalolin tsaro wanda yanzu haka ke cima kasashen Afirika tuwo a kwarya, har ma hakan ya sanya limamai na ta magana a coci da kuma masallatai.

"Kazalika kafewar tafkin Chadi al’amarine mai zaman kansa wanda ke bukatar kulawar da ta dace. Kasancewar shugaba Buhari na magana ne da yawun nahiyar Afrika bai bar yankin na Chadi a baya ba inda ya janyo hankali kan farfado dashi tamkar farfado da tattalin arzikin kasashen dake amfana dashi ne.

Rage fatara da talauci, matsala ce itama mai zaman kanta wadda bayan jawabin shugaba Buhari kungiyar OIC tayi alwashin shiga cikin wadannan matsaloli a kungiyance domin samun maslaha a garesu.” Inji Mallam Garba Shehu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel