Bikin karamar sallah: Hukumar yan sanda ta sanar da hana zirga-zirga a Borno

Bikin karamar sallah: Hukumar yan sanda ta sanar da hana zirga-zirga a Borno

- Rundunar yan sandan jihar Borno ta sanya dokar hana ababen hawa zirga-zirga a yankin

- Abubakar Usman, kakakin rundunar, ya sanar da hakan a wani jawabi a Maiduguri

- Usman yace hanin ya hada da amfani da ababen hawa, kekuna da dabbobi sai dai wadanda ke gudanar da ayyuka masu muhimmanci

Rundunar yan sandan jihar Borno sun sanya dokar hana ababen hawa zirga-zirga a yankin daga karfe 7:00 na safe zuwa 12:15 na rana lokacin bikin Sallah a Maiduguri da yankin karamar ukumar Jere da ke jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Abubakar Usman, kakakin rundunar ne ya fitar da sanarwar a Maiduguri.

Usman ya bayyana cewa “Yan uwa Musulmai na sake bikin karamar sallah a ranakun 4 da 5 ga watan Yuni wanda ke nuni ga kammala azumi 29 ko 30 na Ramadana.

“Sakamakon haka, za a hana zirga-zirgan ababen hawa daga tsakanin 7:00 na safe zuwa 12:15 na rana fara daga ranar 4 ga watan Yuni.

“Hakan zai kasance akan ababen hawa, kekuna da dabbobi sai dai ga ayyuka masu muhimmanci.

“Ana shawartan yan uwa Musulmi da su yi bauta a masallatan kusa da gidajensu sannan su tabbatar sun isa da wuri domin tantancewar tsaro da kuma guje ma sallah cikin gaggawa idan lokaci yayi don ba matakan tsaro hadin kai.

KU KARANTA KUMA: Bikin karamar Sallar: Shugabannin Kirista sun taya Musulmi murna

“Bugu da kari, ana gargadin jama’a musamman matasa masu daukar wukake da sauran muggan makamai zuwa wajen sallah da sauran wurare shakatawa da su guje ma aikata hakan ko kuma su fuskanci doka.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel