Kotu ta umarci rundunar soji ta mayar da wani Janar da ta kora daga aiki

Kotu ta umarci rundunar soji ta mayar da wani Janar da ta kora daga aiki

A ranar Litinin wata kotun ma'aikata dake zamnata a Abuja ta bawa rundunar sojin Najeriya umarnin mayar da manjo janara Nwokoro Ijioma bakin aikinsa.

Mista Ijioma na daga cikin manyan jami'an soji 38 da rundunar soji ta yiwa ritayar dole a shekarar 206.

Da take yanke hukunci, alkaliyar kotun, Edith Agbakoba, ta ce akwai shaidar cewar ba a bi ka'ida ba wajen tilasta Ijioma yin murabus.

Ta ce ba a sanar da Ijioma laifinsa ko gurfanar da shi a gaban kotun sojoji bisa kowacce tuhuma ba kafin a yi masa ritayar dole.

Kazalika ta bayyana cewar ba a bawa Ijioma damar ya kare kansa ko gabatar da wani uzuri ba kafin a sallame shi daga bakin aiki.

Bisa dogara da wadannan hujjoji ne ta sanar da cewar ritayar da aka yi wa Ijioma haramtacciya ce da ta saba wa ka'ida, a saboda haka ba ta da wani tasiri.

Kotu ta umarci rundunar soji ta mayar da wani Janar da ta kora daga aiki

Manjo Janar Ijioma
Source: UGC

Ta bayyana cewar har yanzu Ijioma jami'i ne a rundunar sojin Najeriya.

Alkaliyar ta jingine takaradar ritayar da aka yi wa Ijioma mai dauke da kwanan watan 9 ga watan Yuni na shekarar 2016.

Alkaliyar ta bayar da umarnin mayar da Ijioma kan mukamin da yake kai kafin a sallame shi tare da biyansa dukkan hakkokinsa na tsawon lokacin da aka sallame shi.

DUBA WANNAN: Buhari ya soki masu yiwa talakan Najeriya bukulu a mulkinsa

Sannan ta haramtawa hukumar soji da dukkan wadanda aka Ijioma ya shigar da su kara daukan wani mataki da zai shafi ko da dakatar da hakkokin Ijioma ko kuma muzguna masa.

Ta kuma umarci rundunar soji ta biya shi N200,000 a matsayin kudin da ya kashe wajen shigar da kara a gaban kotun.

Ijioma ya garzaya gaban kotun ne yana neman ta jingine ritayar dolen da rundunar soji ta yi masa a kan korafin cewar ba a bi ka'ida ba wajen yin hakan.

A cikin wadanda Ijioma ya ambata a cikin takardar shigar da kara a gaban kotun akwai shugaban rundunar soji, babban hafsan rundunar sojoji da kuma ministan tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel