NJC ta aminta da ritayar Onnoghen, inji Buhari

NJC ta aminta da ritayar Onnoghen, inji Buhari

-Babu wata ka'ida da aka karya wajen dakatar da Onnoghen a cewar shugaba Buhari.

-NJC ta bada goyon baya gabanin dakatar da tsohon shugaban alkalan, inda a karon kansa ma ya aikawa shugaba Buhari da takardar ajiye aiki.

Shugaba Muhammadu Buhari yayi karin haske akan lamarin tsohon shugaban alkalan Najeriya Jastis Walter Onnoghen.

Daftarin mai dauke da karar da gwamnatin tarayya ta shigar a madadin Buhari da kuma ministan shari’a na kasa na nuna amincewar NJC kan ritayar Onnoghen.

KU KARANTA:Gwamnatin Buhari zata dauki matasan jahar Kano 120,000 aiki na musamman

Daftarin wanda jaridar Punch ta samu ranar Litinin yayi bayanin cewa bisa korafin da hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta shigar, hakan ya zama wajibi ga shugaban alakalan na yayi ritaya saboda ya saba dokar kasa.

Hakan yazo daidai da kudurin kungiyar shari’a ta kasa wato NJC wacce ita ma ke goyon bayan shugaban alkalan ya ajiye aikin nasa ta hanyar fito da batun fili tun ranar 5 ga watan Afirilun 2019.

Babban sakataren ma’aikatar shari’a ta tarayya Mista Dayo Apata ne ya shigar da wannan kara inda yake wakiltar bangaren gwamnatin tarayya a kotun.

Daga bangaren kariya ga shugaban alkalan kuwa sun nemi a dakatar da tabbatar da mukaddashin shugaban alkalan na kasa wato Jastis Tanko Muhammad a matsayin shugaban alkalan na din-din-din.

Inda bangaren ke kalubalantar korafin da cewa matakin gwamnatin tarayya na ranar 25 ga watan Junairun 2019 bai samu amincewar majalisar dattawa da kuma NJC ba.

Kazalika sashen gwamnatin tarayya na kariyar kansu a kan gaskiyar lamarin, inda bangaren ke cewa, “ a daidai lokacin da aka sanar da dakatarwar shugaban alkalan Najeriya akwai takardar da Onnoghen ya aiko ta ajiye aiki a kashin kansa.

“ Hukumar NJC ma tayi irin wannan furucin inda take nuna amincewarta akan hukuncin da CCT ta zartar a kan alkalin.” Inji gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel