Bikin karamar Sallar: Shugabannin Kirista sun taya Musulmi murna

Bikin karamar Sallar: Shugabannin Kirista sun taya Musulmi murna

Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) sun taya musulman Najeriya murnar bikin karamar sallah, wacce ta kawo karshen Ramadana.

Mukaddashin babban sakataren kungiyar, Joseph Daramola, a wani jawabi a jiya, Litinin, 3 ga watan Yuni ya bukaci Musulmi da su ci gaba da tsare kansu daga ayyukan sabon Allah kamar yadda Alkur’ani ya koyar.

“Muna taya daukaci Musulman Najeriya murna yayinda suke bikin sallah sannan muna addu’an Allah ya amsa ibadunsu a wata mai tsarki.

"Muna addu’an kada Allah yasa a fuskanci hare-hare na bama-bamai a yayin bikin.

Muna kira ga yan uwanmu Musulmi da su ci gaba da kare kansu daga ayyukan sabon Allah bayan Ramadan tunda sun tsarkake zuciyoyinsu da azumi. Maimakon haka, su ci gaba da wanzar da zaman lafiya, hadin kai da soyayya a kasar.

"A madadinmu dukka kiristocin Najeriya, muna taya su murna da fatan cewa Allah ya amsa addu’oinsu sannan ya taimaka wa shigabanninmu wajen samun mafita ga matsalolin kasar kafin lokaci ya kure,” inji Daramola.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli a Zamfara jarrabawa ce daga Allah – Wamakko

Ya kuma bukaci dukkanin zababbun shugabanni a dukkan matakai da su rungumi adalci, daidaito da gaskiya a nadenadensu da gwamnatinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel