Hukuncin kotun koli a Zamfara jarrabawa ce daga Allah – Wamakko

Hukuncin kotun koli a Zamfara jarrabawa ce daga Allah – Wamakko

Shugaban kungiyar sanatocin arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayyana hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben jihar Zamfara wanda ya fatattaki APC a matsayin jarrabawa daga Allah.

Kotun ta soke dukkanin kuri’un da aka Jefa wa APC, yayinda ta kaddamar da yan takarar jam’iyyar adawa a matsayin wadanda suka lashe zaben.

Wamakko yace, “jarrabawa ce daga Allah madaukakin sarki kuma Insha Allahu za mu cinye jarrabawar.”

Mai ba sanatan shawara na musamman a harkokin labarai, Bashir Rabe Mani, yace Wamakko ya fadi hakan a lokacin da ya jagoranci wata tawaga domin zo yarar ban girma ga tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar, da mambobin APC a jihar kan hukuncin kotun.

Sanata Wamakko ya bayyana cewa Zamfara da Sokoto tsatso daya ne, inda ya Kara da cewa “duk abunda ya samu daya, toh zai shafi dayan kai tsaye.”

KU KARANTA KUMA: Mai rabon gani badi ya gani: Gwamna Obiano ya sauya ma kwamishinoninsa ma’aikatu

Ya Kara da cewa “wannan ziyarar yan uwantaka ne domin taya ka da dukkanin shugabanni jaje, da mambobin APC gaba daya a jihar.”

A nashi bangaren, Yari ya bayyana cewa hukuncin kotun kolin mukaddari ne daga Allah, wanda baya taba kuskure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel