Mai rabon gani badi ya gani: Gwamna Obiano ya sauya ma kwamishinoninsa ma’aikatu

Mai rabon gani badi ya gani: Gwamna Obiano ya sauya ma kwamishinoninsa ma’aikatu

Gwamnan jahar Anambra, Willie Obiano ya gudanar da tankade da rairaya a gwamnatinsa, wanda hakan ta yi dalilin sauya ma kwamishinoninsa guda shida ma’aikatu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan watsa labaru da wayar da kawunan jama’a na jahar, Mista Don Anuba ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 3 ga watan Mayu, inda yace gwamnan ya sauya kwamishinan muhalli Michael Okonwo zuwa ma’aikatar gidaje, yayin da Obi Nwanko ya koma muhalli.

KU KARANTA: Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Tsohon kwamishinan noma, Afam Mbanefo an daukeshi zuwa ma’aikatar kula da al’amuran matasa da kirkire kirkire a matsayin sabon kwamishina, shi kuwa tsohon kwamishinan matasa, Bonaventure Emenali ya koma ma’aikatar sufiyo da filaye.

Yayin da gwamnan ya sauya ma kwamishinan gidaje, Emeka Ezenwanne ma’aikata zuwa ma’aikatar kula da wuta da ruwa, sai Nnamdi Onukwuba wanda shine tsohon kwamishinan wuta da ruwa ya koma ma’aikatar noma.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sake nada wasu manyan jami’an gwamnatinsa bisa mukamansu, mukaman da suka rike a wa’adin mulkinsa na farko, kamar yadda fadar gwamnatin jahar Kaduna ta sanar.

Gwamnan ya mayar da sakataren gwamnati, Balarabe Abbas Lawal bisa mukaminsa, kamar yadda yayi ma babban sakatarensa, Dakta Salisu Suleiman da kuma babban mashawarcinsa Jimi Lawal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel