Bukukuwan Sallah: An dakatar da zirga zirgan ababen hawa a jahar Yobe

Bukukuwan Sallah: An dakatar da zirga zirgan ababen hawa a jahar Yobe

Bukukuwan Sallah: An dakatar da zirga zirgan ababen hawa a jahar Yobe

Gwamna Mai Mala
Source: Twitter

Gwamnatin jahar Yobe a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta sanar da dakatar da zirga zirgan ababen hawa a ciki da wajen garin Damaturu tun daga karfe 10 na daren Litinin zuwa karfe 10:30 na safiyar Talata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin gwamnan jahar, Abdullahi Bego ne ya bayyana haka a daren Litinin, inda yace Gwamnan jahar ya dauki wannan mataki ne bayan ganawa da shuwagabannin hukumomin tsaro dake jahar.

KU KARANTA: Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

“Wannan mataki ya zama wajibi don samar da ingantaccen yanayi da walwala, tare da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yayin da ake shagulgulan karamar Sallah, kuma gwamna na taya Musulmai murnar zagayowar wannan rana, tare da fatan Allah Ya maimaita mana.” Inji shi.

Idan za’a tuna gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata, 4 ga watan Yuni da ranar Laraba, 5 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin gudanar da shagulgulan karamar Sallah a Najeriya.

Musulmai na duk duniya gaba daya suna gudanar da bikin Sallah karama ne bayan kammala azumin watan Ramadana na tsawon kwanaki 29 zuwa kwanaki 30, kuma ranar Sallar ce ke nuni da an shiga sabuwar watan Shawwal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel