Gwamnatin Buhari zata dauki matasan jahar Kano 120,000 aiki na musamman

Gwamnatin Buhari zata dauki matasan jahar Kano 120,000 aiki na musamman

Akalla matasa marasa aiki yi guda dubu dari da ashirin, 120,000, da suka fito daga jahar Kano ne zasu tagomashin aikin yi daga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni yayin wata ziyara daya kai jahar Kano, inda yace gwamnatin zata kara daukan matasan Kano 120,000 aiki a karkashin tsarin N-Power.

KU KARANTA: Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Osinbajo ya bayyana haka ne ta bakin hadimin shugaban kasa, Isma’eel Ahmad, wanda ya wakilci Osinbajo a taron gudanar da addu’o’I na musamman da wasu mutane da suka ci moriyar tsarin tallafin gwamnatin Buhari suka shirya.

“A cikin shekaru hudu masu zuwa zamu sake daukan matasan Kano 120,000 a karkashin tsarin aikin N-Power, haka zalika zamu kara adadin jama’an dake cin gajiyar tallafin N5000 a kowanne wata daga kananan hukumomi 15 zuwa kananan hukumomi 44.

“Hakanan shima tsarin bashin TraderMoni, zamu baiwa yan kasuwan Kano miliyan biyu bashi mai saukin ruwan a wannan shekarar 2019.” Inji shi.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tsalin bada aikin N-Power da na tallafin Buhari sun bayyana farin cikinsu da dacewa da wannan tagomashi, sa’annan sun yi addu’ar Allah Ya kara ma Buhari lafiya, hikima da tsawon kwana mai albarka don cigaba da aikin alherin da yake yi.

A yanzu haka dai akwai matasa fiye da 18,000 dake cin gajiyar tsarin N-Power a jahar Kano, mutane 51,000 dake samun tallafin naira dubu biyar biyar a duk wata a jahar, ga kuma tsarin ciyar da daliban firamari da kuma bashin Trader Moni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel