Yau take sallah: Sakon Shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya

Yau take sallah: Sakon Shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya

-Shugaba Buhari yayi jawabin goron sallah zuwa yan Najeriya a ranar Litinin.

-Shugaban ya nemi yan Najeriya da cewa kada su damu ba su ba nadamar zabensa, inda ya jaddada cewa hakika zasu ga amfani bashi kuri'unsu da sukayi.

-Kazalika shugaban, yayi amfani da wannan damar domin janyo hankalin yan Najeriya kan cewa su cigaba a kan kyawawan dabi'un da suka koya cikin Ramadana.

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya Litinin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da halayyar da suka kasance akai cikin watan Ramadana.

Ya kuma nuna farin cikinsa bisa gudanar da zabe da akayi a kasar cikin kwanciyar hankali da lumuna, duk da cewa anyita hasashen za’a samu tashin hankali lokacin zaben.

KARANTA WANNAN:Biyu babu: APC ta kori tsohon gwamna Yari daga jam'iyyar

A sakonsa na goron sallah shugaba Buhari ya yabawa hukumar zabe bisa kokarinta na shirya zabe mai inganci a kasar nan. Kana kuma ya jinjinama ‘yan Najeriya a kan juriya da kuma nuna amincewarsu ga da abinda ake kira dimokuradiyya.

“ Kafin zaben 2019 wasu tsirarun mutane sun yita cece kuce kan cewa wannan zabe zai zo da tangarda. Sai ga shi duk da maganganunsu anyi zabe lafiya ba tare da wata fitina ba. Duk wadannan zantukan nasu babu ko guda da yayi tasiri a lokacin zaben saboda anyi komi cikin lumana da kwanciyar hankali.

“ Bari inyi amfani da wannan damar na tunatar da ‘yan Najeriya sadaukar min da kuri’arku da kukayi ba zai tafi a banza ba. Ina mai tabbatar muku da cewa zakuyi na’am da wannan gwamnati tawa.” Inji Buhari kamar yadda hadiminsa ya shaida mana wato Garba Shehu.

A kan Ramadana kuwa shugaban ya nemi jama’a su duba bukatun mutane kafin ra’ayin kawunansu.

“ Watan Ramadana wata ne wanda ke gyara mana imani, don haka ya zama wajibi mu rika amfani da addini wurin aikata abinda yake daidai a koda yaushe. Ya zama dole mu rike abubuwan da muke aikatawa cikin azumi kada mu koma ga aikin barna.” A cewarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel